22 Yuni 2017 - 20:46
Ranar Qudus Ta Dundiya Rana Ce Ta Hadin Kan Al'ummar Musulmi

Mai magana da yawun Rundunar Izzuddin Kassam wanda reshen sojan Kungiyar gwgwarmayar musulunci ta Hamas ne, ya ce ranar Kudus wata dama ce mai girma da musulmin duniya za su hada kawukansu.

mai magana da yawun Rundunar Izzuddin Kassam wanda reshen sojan Kungiyar gwgwarmayar musulunci ta Hamas ne, ya ce ranar Kudus wata dama ce mai girma da musulmin duniya za su hada kawukansu.

Abu Ubaidah wanda ya yi rubuta a sahfinsa na twitter a yau alhamis ya ce; Lokaci ya yi da al'ummar musulmi za su ajiye fadace-fadace a tsakaninsu gefe, su maida hanaklinsu wajen kawo karshen mamayar yan sahayoniya.

A wani gefen, kakakin kwamitin kare kungiyoyin gwagwarmayar palasdinu Khalid Abdulmajid, ya ce; A shekarar bana, ranar kudus tana da nata muhimmanci na musammal domin kuwa wuraren masu tsarki na musulmi da na kiristoci suna fuskantar hatsari mai girman gaske daga yan sahayoniya.

A gobe juma'ar karshe ta watan Ramadana ne dai ranar kudus ta duniya, wacce marigayi Imam Khumain ya ayyana, domin tunatar da musulmi halin da kasar Palasinu ke ciki a karkahsin mamaya.288